*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*


*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*



Gidauniyar *Shettima Foundation Gwandu* hadi da *Bright Capacity Initiatives for Community Enhancement* da kuma *Amuse Hub Solutions Kano* suna sanar da zagayowar shirin koyar da matasa da mata daga *karamar hukumar Gwandu* akan *kiwon kaji, da kiwon kifi, da yadda ake kyankyasan kwai,* mai taken *"AGRI-CLINIC 2018".*

Wanda za'a yi a ranar Asabar 17 da Lahadi 18 ga watan nan a *makarantar Gwandu S Fawa da ke karamar hukumar Gwandu.*

Rajista zai fara ranar Asabar 17 ga watannan daga karfe 8 zuwa 10 na safe a harabar makarantar.

Za'a yi koyarwan aji (lecture) daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana a kullum.

Sannan a yi gwaji (practicals) daga karfe 2 zuwa 4 na rana a kullum.

Harwa yau za'a bada takardun koyarwa, shawarwari akan sana'o'i, bude asusun banki na gida, takardan shedan horaswa, da hanyar samun bashin kama sana'a *DUK A KYAUTA.*

Domin karin bayani, a tuntubi ofishin *TASSHI BUSINESS DEVELOPMENT CENTRE* da ke kusa da ofishin LGEA, a karamar hukumar *Gwandu.*

Allah bada ikon halarta. Ameen

Sanarwa:
*Faruku Bala Gwandu*
Shugaban Shirye-shiryen Shettima Foundation Gwandu

Comments