*PRESS RELEASE*
*Juma'a 15/12/2017*
A yaune *HON. USMAN BUHARI ALI GWANDU* *(Shettiman Garin Gwandu)* da matasan garin *Gora Sullubawa* karkashin mazabar Malisa a karamar hukumar *Gwandu* sukayi zaman tattaunawa domin kawo cigaba da tallafawa al'ummansu.
Wannan zaman ya biyo bayan neman isar da irin taimako da *SHETTIMA FOUNDATION GWANDU* ke gudananrwa musamman ga matasa da gajiyayyu.
Sakataren kungiyar *Alheri Social Club* a garin Gora da ke da membobi sama da dari biyar, Mallam Rayyanu Gora ya nuna matukar farin cikin su akan ziyarar tattaunawan da *HON. USMAN BUHARI ALI GWANDU* ya yi musu.
Mallam Rayyanu ya kara da cewa abun da ke addaban matasan kungiyar sun hada da rashin aikinyi, da rashin tallafi don karatu, da rashin kulawa daga wakilansu.
Don haka sun nemi agaji ta gaggawa bisa ga irin kokarin *SHETTIMA FOUNDATION GWANDU* domin shawo kan matsalolin tasu.
A jawaban masu garin Goran Sullubawan Gabas da ta Yamma, *Alhaji Aliyu* Gora da *Alhaji Garba Gora*, sun yaba wa kokarin *HON. USMAN BUHARI* bisa ga sha'awarsa ta son taimakawa matasa da cigaban al'umma.
Sannan sun kawo koken rashin titin zuwa garuruwansu guda 23, tundaga Malisa ta ratsa Tufara, Gora Kwaccido, Gora Sullubawa, Karangiyar Sanyi, Rinaye har zuwa Dodoru.
Haka kuma sun roki Allah akan Ya bawa gwamnan jahar Kebbi *SEN. ABUBAKAR ATIKU BAGUDU da HON. USMAN BUHARI* kariya da nasarar bukatunsu ta duniya da lahira.
A nasa jawabin, *HON. USMAN BUHARI* ya sanar dasu cewa gwamnatin jahar Kebbi karkashin mulkin *SEN. ABUBAKAR ATIKU BAGUDU* tana aiki tukuru domin samarwa jama'a saukin rayuwa, hanyoyin bunkasa arziki, cigaban noma da kiwo, da sauran aiyuka na cigaban jama'a da gari gaba daya.
*Shettiman Garin Gwandun* ya ce zai tabbatar da akalla matasa da mata dari biyu sun samu tallafin karfafa sana'o'insu da na noma a garuruwan Gora.
Haka kuma ya tabbatar musu da daukan nauyin yin rajistar kungiyarsu a mataki ta jaha tare da turo jami'an banki domin buda musu asusun banki da BVN nan bada jumawa ba.
Ya kara da cewa shirye yake a ko da yaushe domin tallafawa matasa da sauran jama'a kamar yadda maigidansa gwamna *ABUBAKAR ATIKU BAGUDU* ya koyar da su.
*Media Support Team*
*Shettima Foundation Gwandu*

Ina rokon Allah S W A yasamamana shugabanda zai tallafemu da hanya a garin gorah sullubawa,......
ReplyDeletemalisa,gwandu,Kebbi state,Nageria.
Naxeer m Umar gorah sullubawa
ReplyDeleteIna rokon Allah S W A yasamamana shugabanda zai tallafemu da hanya a garin gorah sullubawa,......
ReplyDeletemalisa,gwandu,Kebbi state,Nageria.***†** Naxeer M Umar