A yammacin yau ne *Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu)* ya ziyarci garin *Maruda* a karamar hukumar *Gwandu* domin kai gaisuwar ta'aziyar rasuwar *Malama Hadiza*.
PRESS
RELEASE 2:
Saturday,
17/02/2018
A yammacin
yau ne *Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu)* ya ziyarci garin
*Maruda* a karamar hukumar *Gwandu* domin kai gaisuwar ta'aziyar rasuwar
*Malama Hadiza*.
Marigayiyar
yar shekaru 25 ta rasu ranar Talata da daddare a sanadiyar haihuwa, kuma akayi
jana'izarta ranar Laraba.
Ta rasu ta
bar mijinta *Malam Faruku Bello (Barga)* da yara hudu, mata uku na miji daya
yan shekara 11, 7, 4 da kuma karamarsu da akayi sunan ta yau.
Daga nan
kuma *Hon. Usman Buhari* ya gana da masu garin *Maruda ta Gabas Malam Hassan
Maruda, da Maruda ta Yamma Malam Magaji Dan Alhaji,* da wasu yan siyasa tare da
jama'arsu karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam'iyar APC ta karamar
hukumar *Gwandu, Malam Aliyu Maruda.*
A bayanansu
sun kara jinjina wa kokarin da gwamnatin *shugaban kasa Muhammadu Buhari* da
*gwamna Abubakar Atiku Bagudu* suke yi musamman a gefen noma da kiwo.
Sun kuma
yabi kyawawan halayen *Hon. Usman Buhari* na kulawa da lamurorin jama'a da
kokarin taimakawa matasa.
Sun kara da
cewa duk da yake ba jama'a suka zabe shi, amma dabi'unsa da kokarinsa sunsa
jama'a gaba daya hankalinsu ya dawo kanshi. Sun kuma roki Allah akan Yasa
sabulu ta biya kudin wanka.
Harwayau,
bisa ga sanin halayensa na taimakon addinin musulunci da taimakon al'umma,
kwamitin masallacin Juma'a na garin *Kuyun* karkashin jagorancin maigarin,
*Malam Muhammadu Hakimi* sun kai wa *Shettiman Garin Gwandu* koken rashin
masallacin Juma'a a garin nasu.
An kai
koken ne ta hannun *Sarkin Gabas na Gwandu, Alhaji Bello Haruna Rasheed.*
Wakilin *Hon. Usman Buhari, Malam Nasiru Bala* ya tabbatar musu a wurin
gabatarwan da cewa za'a mika sakonsu kuma Insha'Allah za'a kokarta domin share
musu hawayensu.
Media
Support Team
*Shettiman
Foundation Gwandu*

Comments
Post a Comment