_*"SAI MAI SURE"*_ A yammacin yau ne *Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu)* ya ziyarci garin *Gwabare* da ke cikin *Mazabar Dalijan*.


PRESS RELEASE
Alhamis, 15/02/2018

_*"SAI MAI SURE"*_

A yammacin yau ne *Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu)* ya ziyarci garin *Gwabare* da ke cikin *Mazabar Dalijan*.


A garin ne ya samu kyakyawan tarbo daga masu kananan sanaoi da kasuwanci. In da suka nuna farin cikinsu game da tallafin da *shugaban kasa Muhammadu Buhari* da *gwamna Abubakar Atiku Bagudu* suke bayarwa domin taimakawa talakawa.

*Hon. Usman Buhari* ya kara da bayanai akan shirye-shirye da gwamnati take yi domin taimakawa matasa, yan kasuwa da manoma.

Daga karshe *Shettima* ya saya _suren yin miya_ mai yawa ya rabawa dattawa da samari domin amfani da shi wurin abincin yamma.

Jama'ar garin sun nuna farin cikinsu matuka da wannan lamari, inda suka tabbatar babu wani da ya taba yi musu irin karamcin nan.

An yi addu'a mai tsawo in da aka roki Allah SWA akan Ya baiwa *Shugaban Kasa da gwamnan jahar Kebbi* nasara a zabe na biyu. Shi ma *Shettima* an roki Allah SWA akan Ya cika masa burinsa na alkhairi.

Daga baya yara suka hau kuwa na nuna jin dadi da kiran *_sai mai sure_*

Media Support Team
Shettima Foundation Gwandu

Comments