An yi tsawon kimanin awa uku ana yi wa shugaban kasa *Muhammadu Buhari* da gwamnan jahar Kebbi *Sanata Abubakar Atiku Bagudu* addu'a a garuruwan *Guzabe* ta mazabar *Malisa* da *Kuyu* ta mazabar *Maruda* duk a karamar hukumar *Gwandu.*


PRESS RELEASE2:
Wednesday, 21/02/2018

An yi tsawon kimanin awa uku ana yi wa shugaban kasa *Muhammadu Buhari* da gwamnan jahar Kebbi *Sanata Abubakar Atiku Bagudu* addu'a a garuruwan *Guzabe* ta mazabar *Malisa* da *Kuyu* ta mazabar *Maruda* duk a karamar hukumar *Gwandu.*


An roki Allah akan Ya tabbatar da mulkin shugabannin ne saboda kyakyawar niyarsu da irin ayyukansu na inganta rayuwar jama'a musamman a fannin noma da kiwo.

Haka shima *Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu)* ya samu kyakyawan adduoi da fatan alkhairi a rayuwarsa bisa ga irin hidima da yake yiwa jama'a musamman mutanen karamar hukumar *Gwandu* da kewaye.

An yi adduoin ne a lokacin da *Hon. Usman Buhari* ya kai ziyara garin *Guzabe* domin dubin aikin gyaran rijiyarsu da ta rusga kimanin shekara daya da suka wuce, kuma ya dauki nauyin gyaran rijiyar wanda yanzu haka an kusa kammala aikin ta, amma har anfara amfani da ita.

Rijiyar ita kadai ce ake amfani da ita a garin wadda takai gaba 16 (kafa 96), kuma tayi shekara hamsin da biyar (55) ana amfani da ita.

Haka kuma *Hon. Usman Buhari* ya je garin *Kuyu* ne domin duba koken da suka gabatar na rashin masallacin juma'a, makaranta, ruwan sha, da hanya.

*Hon. Usman Buhari* kuma ya tabbatar musu akan zai kai kokensu inda za'a share musu hawaye.

Media Support Team
*Shettima Foundation Gwandu*

Comments