An shawarci samarin mazabar *Dalijan* akan su cigaba da marawa gwamnatin karamar hukumar *Gwandu* baya karkashin jagorancin *Hon. Shehu Bagudu Dalijan*.
PRESS
RELEASE 1:
Wednesday,
21/02/2018
An shawarci
samarin mazabar *Dalijan* akan su cigaba da marawa gwamnatin karamar hukumar
*Gwandu* baya karkashin jagorancin *Hon. Shehu Bagudu Dalijan*.
*Hon. Usman
Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu)* ya bada shawarar lokacin da
*Kungiyar Matasan Solar, Dalijan* karkashin jagorancin *Abdullahi Sani (280)*
suka gayyaceshi domin ganin aiyukan gayya da sukeyi domin cigaban garin.
*Shettiman
Garin Gwandu* ya kara da cewa karamar hukumar Gwandu tana kokarinta wurin kawo
cigaba a karamar hukumar, a inda yanzu haka an tura mutane shida (6) domin
koyon gyaran rijiyar burtsatse.
*Hon. Shehu
Dalijan* ya tabbatar da cewa yanzu haka ma'aikatan sun fara da gyaran rijiyoyi
uku (3), biyu (2) a *Kurya* da guda daya (1) a cikin *sakatariyar karamar
hukumar Gwandu*, sannan an kayyade gyaran guda ashirin (20) a mazabai guda (10)
cikin karamar hukumar.
Bayan zagayen
dubin aiyukan gyaran hanya tare da *Hon. Usman Buhari* da matasan kungiyar
sukayi ta *Hanyar Sabon Gari* da *Hanyar Kasuwa*, sun kara da cewa zasu cigaba
da aikin gyaran hanya a garkar *Malam Abdullahi Liman* da aikin gyaran gidan
almajirai su kimanin guda dari (100) da ke gidan *Malam Liman Yahaya*
Samarin sun
kara jinjinarsu da goyon bayan gwamnati da tabbatar da cewa babu cin zarafi
cikin tafiyarsu.
Shugaban
matasan jam'iyar APC ta *mazabar Dalijan*, *Malam Umar Idde* shi Ma ya yi
bayanai akan manufofin *Hon. Usman Buhari* musamman ta fannin kokarin matasa
sun samu abun yi a hannu.
A karshe
*Hon Usman Buhari* a madadin kansa da shugaban karamar mulkin *Gwandu Hon.
Shehu Bagudu Dalijan* sun bada gudun mawar naira dubun ashirin (N20,000) ga
matasan domin cigaba da ayyukansu.
*Hon. Usman
Buhari* kuma ya ziyarci wani matashi a garin *Dalijan* da yayi hatsari ya
karye. Allah Ya kara masa lafiya
Media
Support Team
*Shettima
Foundation Gwandu*

Comments
Post a Comment