A yammacin yau ne *Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu)* ya kai ziyara babban asibitin


PRESS RELEASE2:
Sunday, 18/02/2018

A yammacin yau ne *Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu)* ya kai ziyara babban asibitin *Mazabar Kambaza* wurin dubin *Hajiya Muna Kambaza Mai Tuwo* mai kimanin shekaru 85 da aka kwantar. Ya yi amfani da wannan dama domin duba sauran majinyata kuma Ya roki Allah akan Ya basu lafiya.


*Hon. Usman Buhari* ya kuma samu tattauna nasarorin gwamnati da wasu dattijai da matasan garin *Kambaza*. Sun kuma nuna bukatar gwamnati da ta cigaba da waiwayo jiga-jigan yan siyasa da suka wahala domin kara saukin cin nasarar zabe mai zuwa.

*Shettiman Garin Gwandu* kuma ya halarci kwallo zagayen karshe wanda *Young Soccer Committee* suka hada a garin Gwandu, wadda ita ce ta karshe tsakanin yan wasan *Young Pillars* ta yi nasara akan *Junior Fulham* da 1-0.

An bada kyaututtuka da dama kuma *Hon. Usman Buhari* ya dauki nauyin daurin karayar wani dan wasa mai suna *Dawuda* da ya karye a kafa cikin wasa.

Media Support Team
*Shettima Foundation Gwandu*

Comments