PRESS RELEASE
Saturday, 3rd Feb. 2018

A yau Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu) ya halarci daurin auren Malam Bashar Atiku Modibbo da Malama Fatima Sarki wanda aka yi a Gidan Alhaji Sarki a garin Gwandu akan sadaki N50,000.


Shettiman Garin Gwandu ya yi addu'a akan Allah basu zaman lafiya da zuri'a dayyida.

Hon. Usman Buhari kuma ya samu kai ziyara garin Rinaye da garin Malisa karkashin mazabar Malisa in da ya gana da kungiyoyin matasa da kuma yan siyasan garin, karkashin jagorancin Mallam Bala Rinaye, shugaban APC na mazabar Malisa.

A garin Rinaye, Shettiman Garin Gwandu kuma ya ziyarci wurin sana'ar Mallam Muhammad Harande, dan shekara 73 wanda ke sana'ar yin alawar suga daga rakke da suga sama da shekara 45. Anan ya saye alawar mai yawa ya rabawa yara kuma yayi tsaraba da ita.

Daga nan ya garzaya garin Yalango a mazabar Masama inda ya sadu da dumbin masoyansa.

A ko wani gari dai Ya samu kyakyawan yabo da addu'a akan nasara game da duk manufofinsa na kyautatawa da taimakon jama'a.

Haka kuma limamai da shugabannin garuruwan sun roki Allah da Ya baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jahar Kebbi Sen. Abubakar Atiku Bagudu nasarar samun zarcewa a zabe mai zuwa.

Media Support Team
Shettima Foundation Gwandu

Comments