SHETTIMA FOUNDATION SPONSORS BVN REGISTRATION IN GWANDU

PRESS RELEASE
Lahadi 05/11/17

A yau ne aka kaddamar da rajistan BVN da bude asusun banki (Bank Account) a karamar hukumar GWANDU a wani shiri na hadin gwiwar SHETTIMA FOUNDATION GWANDU da TASSHI MICROFINANCE INSTITUTION (TASSHI MFI).


Shugaban karamar hukumar Gwandu, HON SHEHU BAGUDU DALIJAN a wani sako ya tabbatar da cewa wannan shiri ne mai amfani, kuma Ya roki Allah akan Ya bada nasara a cikin shi.

HON. USMAN BUHARI ALI GWANDU (Shettiman Garin Gwandu), shugaban SHETTIMA FOUNDATION GWANDU kuma babban mai taimakawa gwamnan na musamman wajen karfafawa matasa a jahar Kebbi ya gudanar da shirin.

HON. USMAN BUHARI ya shaida cewa wannan aikin na daya daga cikin kudurinshi na tabbatar da cewa duk mutanen Gwandu maza da mata sun samu lambar BVN da asusun banki.

Ya kuma kara da cewa a halin yanzu duk tallafi ko bashin gwamnati a duk matakai ana amfani da BVN da asusun banki ne domin badasu, amma abun da ke cimasa tuwo a kwarya ba komai bane illa mafi yawan mutane musamman matasa da mata da ke karamar hukumar basu da su.

HON. USMAN BUHARI ya kara da cewa TASSHI MFI za ta bude wa duk mai bukata asusun banki domin hada-hadar yau da kullum, haka kuma zata fara yin kananan aiyuka na banki (micro-banking), kuma ya ce nan gaba kadan za'a bude rassa a Dalijan, Malisa da Kambaza domin cimma jama'a cikin sauki.

Bayan asusun TASSHI MFI kuma, ya tabbatar da cewa za'a iya bude asusun banki kai tsaye na bankin ACCESS, FCMB, STERLING ko ZENITH a ofisoshin.

Shettima ya nuna cewa wannan dama ce da ta biyo lasisin da suka samu na matakin MICRO FINANCE INSTITUTION (MFI) bayan aikin da aka fara gudanarwa tin 2009 a karkashin TASSHI BUSINESS DEVELOPMENT CENTRE, kuma akayi amfani da daman domin gwajin hanya (test running) mafi sauki da amfanarwa ga jama'a.


Kaddamarwan ya samu halarta ALHAJI ATTAHIRU RUFAI, da shugaban jam'iyar APC ALHAJI MAHMUDA MUHAMMAD MODE GWANDU wanda ALHAJI LABARAN BOSS ya wakilce shi, da sauran matasa daga dukkan mazabi goma na karamar hukumar GWANDU.

Dukkansu sun nuna jin dadinsu ga shirin kuma suka yi kira ga jama'a akan su yunkuro suyi amfani da wannan dama. Daga bisani suma sun cika takardar sha'awar bude asusun ajiya a TASSHI MFI.

Shettima Media Team
Shettima Foundation Gwandu

Comments