PRESS RELEASE

PRESS RELEASE
Lahadi, 05/11/2017

A yau ne HON. USMAN BUHARI ALI GWANDU (Shettiman Garin Gwandu) ya ziyarci garin GUZABE a karkashin mazabar MALISA, a karamar hakumar GWANDU.

Ziyarar ta biyo bayan koken da mutanen garin GUZABE suka yi ta matsalar samun ruwan sha domin rijiyarsu tayi biga, sanadiyar zaizaya wanda yasa rijiyar ta rufe gaba daya bata fidda ruwa.



Rijiyar ita kadai ce ake amfani da ita a garin, kamar yadda Hakimin garin MALLAM MUHAMMADU DIKKO ya yi bayani.

Ya kara da cewa yanzu haka sai anje fadama mai nisan sama da kilomita daya da jakkai domin samun ruwan sha.

Hakimin ya kara da cewa rijiyar takai gaba 16 (kafa 96), kuma tayi shekara hamsin da biyar (55) ana amfani da ita.

Hon.Usman Buhari wanda yaje garin da kansa, ya tabbatar wa da jama'ar Guzabe akan SHETTIMA FOUNDATION GWANDU zata daukin nauyin gyaran rijiyar cikin lokaci kalilan.

Haka kuma Hon. Usman Buhari, wanda shine mai taimaka wa gwamnan jahar Kebbi na musamman akan hanyoyin karfafawa matasa, ya kara tabbatar wa da mutanen garin cewa gwamnatin jahar Kebbi karkashin mulkin Senator Abubakar Atiku Bagudu tana nan tana aiki tukuru domin samarwa jama'a saukin rayuwa da bunkasa kananan yan kasuwa, manoma da makiyaya.

Ya kara kira garesu da su tabbatar mutanensu suma sun fito kansu da kwarkwatansu domin amfana da wadannan hanyoyi.

Media Support Team
Shettima Foundation Gwandu

Comments