Juma'a, 10/11/2017
A yau ne Hon. Usman Buhari Ali
Gwandu (Shettiman Garin Gwandu) ya ziyarci babban filin kwallo da ke Birnin
Kebbi, wurin da ake gasar kwallon General Tukur Burutai.
Duk da yan wasan Gwandu Pillars
sun fadi a wasan da suka yi da yan kwallon....... Amma ya tabbatar musu da cewa
sunyi namijin kokari na kawo wa mataki biyun karshe
Hon. Usman Buhari kuma Ya kara da
cewa zai yi kokarinsa domin ganin yadda za'a farfado da wasanni musamman na kwallo
a Gwandu.
Ya yi ziyarar ne tare da babban
maitaimakawa gwamna a fannin matasa da wasanni, Hon. Nafiu Saidu Magini.
Hon. Nafiu Magini ya tabbatar da
cewa kwallo na daya daga cikin wasannin da ke jawo hankalin matasa, don haka ya
kamata ace masu hannu da shuni su kama musu.
Media Support Team
Shettima Foundation Gwandu


Comments
Post a Comment