Press Release

Alhamis, 02/11/17

A yau ne Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu) kuma Shugaban Shettima Foundation Gwandu ya halarci daurin auren diyar tsohon shugaban jam'iyar APC ta mazabar Kambaza, Mallam Usman Kambaza, Mallama Hussei Usman da Mallam Yusufu Muhammad wanda aka yi a garin Kambaza kuma akan sadaki naira dubu talatin da biyar.






Haka kuma, a wani zama da Shugaban APC na Kambaza da matasan Kambaza sukayi da Hon. Usman Buhari, sun yi godiya ga irin taimakon da yake yiwa matasan Kambaza musamman wurin tallafi da yake bayarwa.
Shugaban APC na Kambaza, Mallam Aliyu Abdullahi Kambaza ya kara da cewa fatan mutanen Kambaza shine Allah Ya bada sa'a ga masu kaunar jama'a, musamman matasa.

Haka ma kansila mai wakiltar Kambaza, Abdulnasir Yahaya shima ya kara da cewa hakika Hon. Usman Buhari ya na taka rawa matuka domin tabbatar da cigaban matasan Gwandu gaba daya. Kuma ya roki Allah da ya ida nufin alkhairi gareshi.

Da yake maida jawabi, Hon. Usman Buhari ya roki Allah akan Ya bawa ma'aurata zaman lafiya.

Kuma ya yi godiya da yabo da karramawa da jama'ar Kambaza suka yi masa.

Shettima ya kuma tabbatar da cewa zai cigaba da samarwa jama'a da matasa da hanyoyin cigaba da bunkasa arziki.

Media Support Team
Shettima Foundation Gwandu

Comments