PRESS RELEASE
Talata, 14/11/2017
A yau ne Youth Leaders na mazabi goma a karamar hukumar Gwandu suka ziyarci Hon. Usman Buhari Ali Gwandu, kuma shugaban Shettima Foundation Gwandu.
Shugabannin na mazabanne karkashin jagorancin APC Youth Leader na karamar hukumar Gwandu, Dan Alhaji Gwandu sun tabbatar da nasabar ziyararsu akan kara jinjinawa Hon. Usman Buhari akan irin namijin kokarin da yake yi akan kawo cigaban matasan karamar hukumar Gwandu, da jahar Kebbi gaba daya.
Dan Alhaji ya kara da cewa Hon. Usman Buhari ya nuna shi mai iyawa da lalurorin matasa ne domin kuwa ba'a taba samun matashi mai kishin matasa ba a Gwandu kamarsa.
Haka kuma shugaban matasa na Dalijan, Umaru Idde Dalijan shima ya kara jinjina wa Hon. Usman Buhari a inda yace matasa da dama a Dalijan da kewaye sun amfana da sanaoin da Hon. Usman Buhari yasa aka koyawa matasa.
Dukkannin shugabannin dai sun tabbatar wa da Hon. Usman Buhari akan a shirye suke domin kama masa duk wani hanya da ya kawo don taimakawa matasa.
Haka kuma sun kara tabbatar da goyon bayansu gareshi da nuna sha'awarsu akan ya fito takara a zabe mai zuwa, domin kuwa sun tabbatar da cewa zai amfani karamar hukumar Gwandu fiye da kima.
A jawabinsa, Hon. Usman Buhari ya yi musu godiya na ziyarar bazata da suka yi masa, da kuma yaba ayyukan da yake yi wa jama'a, musamman matasa.
Ya kara da a cewa yana yiwa Allah godiya, kuma yana kara godiya ga mai girma gwamnan jahar Kebbi, Senator Abubakar Atiku Bagudu da ya bashi daman yin aikin da ya saba yi.
Haka kuma Ya tabbatar musu da cewa batun maganar takara, a cigaba da rokon Allah akan zabin abu mafi alkhairi gareshi da jama'ar Gwandu gaba daya.
Ya kuma kara da cewa yanzu abunda ke gabansa ba komai bane illa cigaba da kamawa gwamnati domin samarwa da matasa hanyoyin ayyukan yi da ta inganta sanaoinsu da sauran ayyukan hannu.
Ya kuma tabbatar musu da cewa akwai wasu shirye-shirye da za'a gudanar nan bada jimawa ba domin cimma kudurorin gwamnati ga karfafawa matasa.
Media Support Team
Shettima Foundation Gwandu

Comments
Post a Comment