PRESS RELEASE
26/11/2017

SHETTIMA FOUNDATION GWANDU TA YI RABON HULUNAR SANYI GA YARAN MAKARANTA

A yau ne uwargidan HON. USMAN BUHARI ALI GWANDU (Shettiman Garin Gwandu) kuma shugaban Shettima Foundation Gwandu, HAJIYA ZARA'U GWANDU ta kai ziyara makarantar matakin farko ta Umaru Cheberu (UMARU CHEBERU NURSERY SCHOOL) dake shiyar Ilellah, a garin Gwandu.
Ida tasamu rakiyar matar mataimakin shugaban karamar hukumar mulki ta Gwandu HAJIYA NAFISA AHMED (KALCHA)
A ziyar ne HAJIYA ZARA'U ta yi rabon hulunar sanyi kimanin guda dari (100) ga yaran aji daya (Nursery 1 A&B).


Daga bisani kuma HAJIYA ZARA'U ta yi zaman tattaunawa tare da kungiyar uwaye mata ta makarantar (MOTHERS ASSOCIATION) a inda suka bayyana mata matsalolinsu.

HAJIYA ZARA'U ta ce ziyarar nata na da nasaba ne ga karin karfafawa maigidanta HON. USMAN BUHARI ALI GWANDU wajen taimakawa jama'a musamman mata, yara da marasa karfi.

Ta bayyana cewa a shirye suke domin tabbatar da tallafi ga mata da matasa domin bunkasa arzikinsu ta hanyar samar musu sana'o'i da hanyoyin samun kudin shiga.

Ta kara da cewa kusan shekara takwas kenan kungiyar SHETTIMA FOUNDATION GWANDU da ta BRIGHT CAPACITY INITIATIVES suke tallafawa mata da matasa ta koyar da sana'o'in hannu da bada bashi a karamar hukumar ta Gwandu ga mata masu karamin karfi.

A nata jawabin, Shugabar kungiyar uwaye mata ta makarantar, MALLAMA SAUDATU MUHAMMAD ta nuna farin cikin uwaye da yaransu domin irin karramawa da taimakon da Hajiya Zara'u da maigidanta ke yi wa jama'a a Gwandu da kewaye.

A inda ta tabbatar da cewa ita kanta da yan'uwanta da dama sunci gajiyar koyan sana'o'i kala-kala da kuma tallafin bashin.

Ta kara da cewa duk Gwandu babu wata kungiya dake fafutuka akan gudanar da shirye-shiryen tallafawa uwaye mata, yara, matasa da nakasassu kamar yadda SHETTIMA FOUNDATION GWANDU take yi.

Daga karshe anyi addu'an Allah saka musu da alkhairinsa bisa ga kudirinsu akan irin hidimar da suke yi da jama'a.

Media Support Team
Shettima Foundation Gwandu

Comments