Press Realease

PRESS RELEASE
Assabar, 04/11/17

A yau ne Hon. Usman Buhari Ali Gwandu (Shettiman Garin Gwandu) kuma Shugaban Shettima Foundation Gwandu ya halarci daurin aure a garin Dalijan.

An daura auren Bilyaminu Altine da Zainab Abdulrazaq, da na Junaidu Abdulrazaq da Hasiya Shehu, da na Bashar Abubakar da Farida Altine, da kuma na Abbas Shehu da Sadiya Arzika duk akan sadaki naira dubu hamsin kowanne.



Sai kuma an daura auren Usman Aliyu da Zinatu Shehu akan sadaki naira dubu hamsin da biyar.

Taron auren sun samu halartar Shugaban karamar hukumar Gwandu, Hon. Shehu Bagudu Dalijan, Dan Majalisa mai wakiltar Gwandu Hon. Faruk Muhammad, da dai sauran manyan baki.


Daga nan kuma Hon. Usman Buhari ya zarce zuwa Tari domin yiwa Hon. Shehu Tari barka da Allah kyauta bisa ga mukamin da ya samu na mai bawa gwamna shawara.

Harwa yau, Hon. Usman Buhari ya biya asibitin Tari domin duba aikin gyaran asibitin garin Tari.

Daga nan Shettima da Hon. Tari suka garzaya garin Yole mai Miya, a inda Hakimin garin, Mallam Labbo Hakimi ya bayyana cewa babbar matsalarsu ita ce rashin ruwan sha.

Shettiman Garin Gwandu yayi rokon Allah akan Ya ba ma'auratan zaman lafiya gaba daya kuma Ya basu ikon daukan nauyin da Ya daura musu.

Ya kuma yaba ga aikin da ake yi na gyaran asibitin Garin Tari.

Kuma ya tabbatar ma da mutanen Yole me Miya akan zai turo masu aikin ruwa domin duba matsalar.

Media Support Team
Shettima Foundation Gwandu

Comments

Post a Comment