SHETTIMA FOUNDATION LAUDS APC

A YAUNE Talata 3/10/2017 kungiyar matasa ta garin Gumbai a mazabar Maruda da ke karamar hukumar GWANDU ta gudanarda aikin gayya na gyaran babar hanyar garin.

Aikin gayyar dai tasamu halartar Chairman na APC na karamar hukumar Gwandu, ALHAJI MAMUDA GWANDU , kansila mai wakiltan Maruda, HAJIYA SHARIFIYA.



Hon. Usman Buhari Ali Gwandu, kuma Shugaban SHETTIMA FOUNDATION GWANDU, shi ma ya aika gudunmawarsa ga matasan domin karfafa musu akan aikin da suka dauko, wanda USMAN LADAN da FARUKU BALA suka wakilci shi.

Daya daga cikin wakilan Hon. Usman Buhari, Usman Ladan ya tabbatar da cewa wannan na daya daga cikin kokarin da kungiyar SHETTIMA FOUNDATION GWANDU ta ke yi wurin tabbatar da kawo cigaban al'umma.

Shugaban APC na karamar hukumar Gwandu, Alhaji Mahmuda Gwandu ya yi godiya ga taimakon da Hon. Usman Buhari Ali Gwandu ya bayar domin karfafa aikin.

Ya kara kira ga jama'a akan su dinga bada gudunmawarsa ga aiyukan cigaba da mutane suke daukowa.

Kansilar Maruda wanda ita ma ta samu halarta, ta kara kira ga matasa da su rungumi aikin gayya domin kawo cigaba ga garuruwansu.

Comments